Alhamis 2 Yuli 2026 - 19:28
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (49) | Mahdawiyya A Cikin Alkur'ani (Sashe na Farko)

Hauza/ Alkur'ani ya yi magana ne ta bai-daya game da bayyana da juyin juya halin Hazrat Al-Mahdi (A.F), kuma ya yi bushara game da kafa gwamnatin adalci ta duniya da kuma nasarar mutanen kirki (ibadus salihin). Masu tafsirin Shi'a da wasu daga cikin masu tafsirin Sunnah sun ɗauki irin waɗannan ayoyi a matsayin waɗanda ke da alaƙa da Hazrat Al-Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanarsa).

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya rawaito cewa, ana gabatar da wannan jerin darussa na Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yaɗa ilimin da ke da alaƙa da Imamin Zamani (Allah ya gaggauta bayyanarsa), zuwa gare ku masu karatu.

Tunanin "Mahdawiyya" a Musulunci yana da asali na Alkur'ani, kuma wannan littafi mai tsarki, da cikakken tabbaci, ya yi wa dukkan bil'adama albishir da nasarar ƙarshe ta "Gaskiya" akan "Ƙarya".

Alkur'ani ya yi magana ta bai-daya game da bayyana da juyin juya halin Hazrat Al-Mahdi (A.J) kuma ya yi busharar kafa gwamnatin adalci ta duniya da nasarar mutanen kirki. Masu tafsirin Shi'a da wasu masu tafsirin Sunnah — bisa dogaro da ruwayoyin Ahlul-Baiti (A.S) da ra'ayoyin malaman Musulunci — sun ɗauki waɗannan ayoyi a matsayin waɗanda suka shafi Hazrat Al-Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanarsa).

A cikin wannan gurbi, daga cikin dukkan ayoyin Alkur'ani da suka shafi batun Mahdawiyya kuma suka fi fitowa fili a cikin wannan tattaunawa, za mu kawo tare da yin bincike akan ayoyi kalilan kacal.

Domin shiga cikin tattaunawar, da farko ya zama dole mu fahimci ma'ana da manufar wasu kalmomi:

1. Tafsir (Fassarar Ma'ana)

"Tafsir" ya fito ne daga kalmar "Fasara", wanda ke nufin bayyanawa da fito da abu fili. Kuma a "a fannance" (اصطلاح) yana nufin: "Yaye duhu daga kalma mai wahala da sarkakiya", kuma ya haɗa da "kore duhun da ke tattare da abin da magana ke nunawa".

Tafsir yana kasancewa ne a inda akwai wani nau'in sarkakiya ko rashin fitowa fili a cikin kalma, kuma wannan yana haifar da rashin fahimtar ma'ana da abin da maganar ke nufi, wanda hakan ke buƙatar ƙoƙari mai yawa don warkar da shi.

Kamar yadda fahimtar wasu ayoyin Alkur'ani ke kasancewa a ɓoye ga gama-garin mutane, babu makawa suna buƙatar bayani da yaye musu labule, kuma wannan babban aiki yana wuyan mutanen da ke da cancanta da ikon yin hakan kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya amince da su.

2. Ta'awil (Tawili)

Ta'awil ya fito ne daga "Awl", wanda ke nufin komawa ga asali. Ta'awil ɗin wani abu yana nufin mayar da shi zuwa ga mazauninsa ko asalin madogararsa; kuma ta'awil na kalma mai kama da juna (Mutashabih) yana nufin fassara bayyanannen lafazi ta yadda zai koma ga tabbatacciyar ma'anarsa ta gaske.

Wannan kalma ta zo a cikin Alkur'ani da ma'anoni guda uku:

 * "Fassara bayyananniyar kalma ko aiki mai rikitarwa" ta hanya madaidaciya wacce hankali zai karɓa kuma ta dace da ruwayoyi na addini. (Al-Imran/ 7)

 * "Fassarar mafarki"; Ta'awil da wannan ma'ana ya zo sau takwas a cikin Suratu Yusuf.

 * "Sakamako ko ƙarshen aiki"; a kan wannan mizanin, ta'awil ɗin wani lamari yana nufin abin da wannan lamarin yake karewa a kansa. (Al-Kahf/ 78)

Ma'ana ta huɗu — wacce ba ta zo a cikin Alkur'ani ba, amma tana cikin kalaman magabata — ita ce: Cire wata ma'ana ta bai-ɗaya mai faɗi daga ayar da aka saukar a kan wani takaitaccen lamari na musamman. Daga ta'awil da wannan ma'ana, wani lokacin ana kiransa da "Baɗn" (Ciki); wato ma'ana ta biyu kuma a ɓoye wacce ba a samun ta daga bayyananniyar ayar. Sabanin "Zahr" (Bayan); wato ma'ana ta farko wacce aya bayyananniya  ke nuna ta dangane da yadda aka tsara kalmar da amfani da ita.

Wannan ma'ana tana da faɗi sosai kuma ita ce ke tabbatar da cewa Alkur'ani na kowa da kowa ne kuma na kowane lokaci; domin idan ba a ciro ma'anoni na bai-ɗaya daga takamaiman lokaci ba, da yawancin ayoyin Alkur'ani sun zama marasa amfani, kuma ba za su kasance da wani amfani ba in ban da ladan karanta su da rera su.

Babu shakka a cikin Alkur'ani akwai ayoyi masu rikitarwa (Mutashabihat) waɗanda dole ne a yi musu tawili; amma ba kowa ne ya sani ba sai Allah da kuma waɗanda suka zurfafa a cikin ilimi. (Al-Imran/ 7)

Ta'awil yana da sharuɗɗa da ma'aunai waɗanda aka yi bayaninsu a cikin littattafan da suka dace.

3. Taɗbiƙ (Dacewa ko Amfani da aiki)

A cikin ayoyin Alkur'ani, an bayyana abubuwa da yawa da lafazi na bai-ɗaya (Am), wanda a kowane lokaci, ana iya amfani da shi ko ya dace da wasu gungun mutane. Wani lokaci kuma, lafazin ayar na "musamman" ne (Khas), amma ma'anarta ta "dai-ɗaya" kuma ta haɗa da mutanen da irin wannan aiki ya fito daga gare su.

Duba da waɗannan nukuda da aka ambata, za mu tattauna wasu ayoyin da suka shafi Imam Al-Mahdi (A.F) da kuma juyin juya halinsa na duniya: ...

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ciro ne daga littafin "Darsnameh-ye Mahdaviyyat" wanda Khodamurad Salimiyan ya rubuta, tare da ɗan gyara kadan

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha